4 Disamba 2019 - 04:26
An Kashe Sojojin Kasar Syria Biyu A Arewacin Kasar

Rahotannin da su ke fitowa daga kasar ta Syria sun ce sojojin kasar ta Syria biyu sun mutu ne sanadiyyar wani hari da sojojin Turkiya su ka kai a garin Ayn Isa da ke arewacin kasar.

(ABNA24.com) Rahotannin da su ke fitowa daga kasar ta Syria sun ce sojojin kasar ta Syria biyu sun mutu ne sanadiyyar wani hari da sojojin Turkiya su ka kai a garin Ayn Isa da ke arewacin kasar.

Kamfanin dillancin “Hawari” na Kurdawan Syrai ya ambaci cewa; Sojojin na kasar Turkiya sun yi amfani da tankokin yaki ne wajen kai harin akan sansanonin sojojin Syria da su ke garin Haymar mai nisan kilo mita 15 daga Ayn Isa a arewacin gundumar Riqqah.

Majiyar ta kuma ce; baya ga sojoji biyu da su ka kwanta dama, wasu Karin sojojin 3 sun jikkata.

Kamfanin dillancin labarun na Kurdawa ya kuma kara da cewa; Su ma sojojin Syria sun mayar da martani akan sansanin sojan Turkiya da ke kauyen Abu Kharzah, da hakan ya yi sanadin jikkatar jami’in sojan Turkiya daya.

Syrai ta girke sojojinta a yankuna daban-daban na gundumomin Hasaka da Riqqah domin fuskantar kusten da sojojin Turkiya su ka yi a kasar saboda fada da kungiyoyin kurdawa.



/129